Revelation of John 6

Hatimai

1Na ƙalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” 2Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara.

3Saʼad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” 4Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yǎ ɗauke salama daga duniya yǎ kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.

5Saʼad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. 6Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na shaʼir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”

7Saʼad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” 8Na duba, can a gabana kuwa ga koɗaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya.

9Saʼad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. 10Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai tsarki da kuma mai gaskiya, har yaushe za ka shariʼanta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” 11Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ʼyanʼuwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.

12Ina ƙallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, 13taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ʼyaʼyan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure saʼad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. 14Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.

15Saʼan nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ʼyantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. 16Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! 17Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”

Copyright information for HauSRK